Monday, 15 October 2018

Me baiwa shugaba Buhari shawara ya bayyana yanda Buhari zai lashe zabe a 2019

Me baiwa shugaban kasa shawara a kan sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmed ya bayyana cewa, yawan wanda suka yi rigistar zabe kamar yanda hukumar zaben ta INEC ta bayyana sune kamar haka:

Arewa maso yamma: 18,504,984
Kudu maso yamma: 14,626,800
Kudu maso kudu: 11,101,093
Arewa ta tsakiya: 10,586,965
Arewa maso gabas: 9,929,105
Kudu maso gabas: 8,293,093

Ya kara da cewa, Arewa maso yamma, Kudu maso yamma da Arewa maso gabas duk na Buharine.


Ya kuma ce yankin Arewa maso yamma me mafi yawan kuri'u na Buharine sai me bishi, Kudu maso yamma shi kuma na Osinbajo ne. Shikenan.

No comments:

Post a Comment