Tuesday, 9 October 2018

Me zai faru a majalisa bayan ta koma hutu

Majalisar dokokin Najeriya za ta dawo zama bayan wani hutu da ta je tun ranar 24 ga watan Yuli.


Tun a watan Satumba majalisar ta yi alkawarin komawa aiki amma ta dage zaman saboda zabubbukan fitar da gwani na jam'iyyun siyasa, kamar yadda ta bayyana.

Kakakin majalisar wakilai Hon Abdulrazak Namdaz ya shaidawa BBC cewa akwai muhimman batutuwa da za su duba a ranar da suka koma aiki.

Ya ce babban muhimmin batu shi ne game da dokar zabe tare da kuma duba batun kasafin kudin hukumar zaben kasar INEC.

Sannan ya ce akwai batun duba basussukan da shugaban kasa ya ke neman majalisar ta amince.

An samu sauyin sheka tsakanin 'yan majalisar cikinsu har da shugabanni, lamarin da ake ganin zaman majalisar zai haifar da wani yanayi sabo a zauren majalisun biyu.

Kuma ana ganin sauya shekar na iya tasiri ga muhimman batutuwan da majalisar ta ce za ta diba wajen amincewa da su.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment