Sunday, 21 October 2018

Mene ne dalilin hana Atiku shiga Amurka?

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya nemi izinin shiga Amurka, amma an hana shi.


Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Jimeh Saleh bayan wata ziyara da ya kai ofishin BBC da ke Landan a watan Afrilun bana - wato kafin tsayar da shi a matsayin dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Ya musanta cewa an yi gwanjon wani gidansa na Amurka, inda ya ce gidan matarsa ne, kuma "ita ta sayar da gidanta ta karbi kudinta."

Haka kuma yace shine ya siyawa matartashi gidan kamar yanda yake saiwa sauran matanshi a Najeriya domin shi baya bukatar gida.

Atiku ya kuma kara da cewa ai ba lallai sai mutum yaje kasar ta Amurka ba kuma basu bayyana mishi dalilin da yasa suka hanashi shiga kasar ba kumama bashi da wani kasuwanci a kasar.

No comments:

Post a Comment