Saturday, 13 October 2018

Messi be kamata ya shugabanci 'yan wasa ba sau 20 yake shiga wanka kamin a fara wasa

Kasar Argentina ta baiwa Lionel Messi Kyaftin din 'yan wasan kwallonta saidai tsohon dan wasan kasar, Diego Maradona na ganin Messin be dace da wannan aiki ba.A wata hira da yayi da wani gidan talabijin kamar yanda Marca ta ruwaito, Maradona ya bayyana cewa ta yaya za'a baiwa mutumin da duk kamin a fara wasa sai ya shiga wanka sau 20 jagorancin 'yan wasa?

Yace Messi kwararren dan wasane kuma a haka ya kamata a barshi amma shugabanci be dace da shiba, ya kara da cewa, kuma wani lokacin fa kamin yayi magana da 'yan wasa ko kuma me horas da 'yan wasan sai ya buga wasan kwamfuta dan haka bai dace da shugabanci ba.

Maradona yace Messin ya fi buga kwallon azo a gani idan yana kungiyarshi ta Barcelona fiye da idan yana gida Argentina.

No comments:

Post a Comment