Sunday, 21 October 2018

Messi ya ji rauni a wasan da Barca ta doke Sevilla 4-2

An yi waje da Lionel Messi sakamakon raunin da ya ji a hannunsa na dama jim kadan bayan da ya ci wa Barcelona bal a karawar da ta doke Sevilla 4-2, kwana 8 kafin gumurzunsu na hamayya da Real Madrid, yayin da zai yi jinyar mako uku.


Dan wasan na Argentina ya kasance cikin tsananin ciwo bayan da ya fado a kan hannun nasa sakamakon karo da suka yi da Franco Vazquez na Sevilla.

An ga alamun yana jin zafin raunin a lokacin da za a fitar da shi daga fili a minti na 26.
Kafin ya ji raunin ne ya ci wa Barcelona bal ta biyu a minti na 12, bayan tun da farko ya saka wa Philippe Coutinho ya fara daga raga minti biyu kacal da shiga fili.

Bayan an dawo kashi na biyu na wasan ne Suárez ya ci ta uku da fanareti bayan da golan Sevilla ya kayar da shi a minti na 63.

Sevilla ta samu daya ta hannun Sarabia a minti na 79, kafin kuma Rakitic ya ci wa Barcelona ta hudu cikin minti na 88, sakamakon da bai yi nisa ba Muriel ya kara ci wa bakin bal ta biyu bayan cikar minti 91.

Da wannan sakamako Barcelona ta zama ta daya a teburin na La Liga da maki 18 a wasa 9, Alaves na bi mata baya da maki 17, sai Sevilla ta uku da maki 16, yayin da Atletico Madrid take matsayi na hudu ita ma da maki 16, amma da bambancin yawan kwallo 3 Sevillan.

Bayanai sun nuna cewa Messin mai shekara 31, zai yi jinyar tsawon mako uku, yayin da suke fuskantar wasanni masu tsanani da suka hada da na Zakarun Turai, da Inter Milan a tsakiyar mako, da kuma karon-batta da Real Madrid a karshen mako.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment