Saturday, 27 October 2018

Mohamed Salah yaci wa Liverpool kwallo ta 51

Tauraron dan kwallon kafar Liverpool, Mohamed Salah ya ci wa kungiyar tashi kwallo ta 51 a yau Asabar a wasan da suka buga da kungiyar Cardiff.


Bayan cin kwallon da yayi, Salah ya kuma bayar da taimako aka ci karin kwallaye biyu ciki hadda wadda Sadio Mane yaci.

Mane yaci kwallaye biyu sai kuma Xherdan Shakiri ya ci ta hudu, suma Cardiff sun saka kwallo 1, wanda a haka aka tashi wasan 4-1.

Masu sharhi dai na ganin Salah din zai ci gaba da cin kwallaye nan gaba, a kakar wasan da ta gabata dai shine ya lashe kyautar takalmin zinare a matsayin wanda yafi yawan kwallaye a gasar Firimiya.


No comments:

Post a Comment