Friday, 5 October 2018

Mutane dubu 1,558 girgizar kasa ta kashe a tsibirin Sulawesi na Indonesiya

An sake fitar da sabona dadin mutanen da girgizar kasa ta kashe a tsibirin Sulawesi na kasar Indonesiya inda a yanzu aka tabbatar da mutuwar mutane sama da dubu 1500.


Sanarwar da Hukumar Magance Annoba ta Indonesiya ta fitar ta ce, a yanzu mutanen da ibtila'in ya kashe sun kai dubu 1,558.

Girgizar kasa ta afku a tsibirin Sulawesi a yanki mai tsayin kilomita 27 kuma Hukumar Bincike Kan Yanayin Kasa ta AMurka ta ce, girgizar na da karfin awo 7.5.

Amma majiyoyin yankin sun ce, girgizzar na da karfin awo 7.4.

Bayan afkuwar girgizar kasar Tsunami ta afku a garuruwan Dongala da Palu da zurfin mita 3 zuwa 6.

A karshen watan Yuli zuwa farkon Agustan bana girgizar kasa masu karfin awo 6.3 da 6.9 sun afku a tsibirin Lombok na Indonesiya inda lamarin ya shafi sama da mutane dubu 450 yayin mutum 563 suka mutu.

Indonesiya na yankin tekun Pacific inda a shekarar 2004 girgizar kasa mai karfin awo 9.1 ta afku tare da janyo Tsunamin da ya kashe mutane sama da dubu 230,000.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment