Saturday, 27 October 2018

Na samu ribar N60.2m cikin shekaru 3>>Atiku ya fadawa INEC

Dan takarar shugbancin kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewar ya tara makuden kudi N60.2 cikin shekaru uku kamar yadda ya rubuta cikin takardun da ya mikawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa (INEC).


Ya kuma bayyana cewar ya biya harajin N10.8 ga gwamntain tarayya daga shekarar 2015 zuwa 2017 kamar yadda ya hada tare da fam din takarar shugabancin kasar sa.

Atiku dai yana daya daga cikin manyan Attajiran Najeriya kuma ya yi alkawarin zai habbaka tattalin arziki ta samar da ayyuka a Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

Sai dai adadin na N60.2 miliyan da ya ce ya tara cikin shekaru uku ya bawa mutane da yawa mamaki.

Takardun da dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar PDP ya mika wa INEC ya nuna cewar takarda shaidar kammala Diploma a fanin Shari'a daga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 1969 itace takardan karatunsa mafi girma.

A bangarensa, shugaba Muhammadu Buhari ya mika fom din takararsa inda ya sake jadada cewar takardun karutunsa suna wajen hukumar Sojin Najeriya.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment