Wednesday, 31 October 2018

Ni da Messi ne kawai 'yan wasan da suka yi tashe na tsawon shekaru 10>>Ronaldo

Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa da wuya a samu 'yan kwallon da zasu iya yin irin bajintar da shi da Messi suka yi cikin shekaru 10.


Ya bayyana hakane a wata hira da yayi da wata kafar watsa labaran wasanni ta kasar Faransa inda aka tambayeshi wa yake ganin zai ci kyautar Ballon d'Or ta bana?

Ronaldo ya bayar da amsar cewa, 'yan wasa nawa zasu iya yin tashe na tsawon shekaru goma? zaka iya kirgasu da yatsunka, ni ne kawai da Messi.

Ya kara da cewa, yasan nan da shekaru masu zuwa dole ne a samu canji amma dai zasu zuba su gani.

No comments:

Post a Comment