Saturday, 27 October 2018

Nima takarduna na hannun sojoji>>Dan takarar shugaban kasa Al-Mustafa

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PPN, Major Hamza Al-Mustafa ya bayyana wa hukumar zabe, INEC cewa takardun makarantarshi na hannun hukumar sojin kasarnan.


A doka akwai takardun da 'yan takara ya kamata su mikawa INEC ciki hadda takardun kammala makaranta amma a cikin wasikar da ya aikewa INEC din wadda jaridar The Cable tace ta gani, Major Hamza Almustafa ya bayyana cewa takardunshi na hannun sojoji duk da umarnin da kotu ta bayar na cewa a bashi abinshi amma sun kiya.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ma ya bayyana cewa takardun makarantarshi na hannun hukumar sojan kasarnan.

Saidai kokarin da The Cable ta yi na jin ta bakin hukumar sojin akan wannan batu ya ci tura.

No comments:

Post a Comment