Tuesday, 16 October 2018

Obasanjo ya fadi yadda gwamnatinsa ta azurta Dangote da wasu manyan attajirai

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewar sauye-sauye a fanin banki da gwamnatinsa ta yi ne ya bawa bankuna damar bawa Aliko Dangote da sauran 'yan kasuwa bashin da ya yi amfani dashi wajen bunkasa kasuwancin su.

Obasanjo ya yi wannan furucin ne a yayin da ya jawabi a wata lekca ta Babacar N'daiye da bankin tallafawa masu shigo da fitar da hajja daga Africa (Afrieximbank) ta shirya a yayin da ake gudanar da taron IMF/Bankin Duniya a Bali da ke kasar Indonesia.

"A Najeriya, Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya fada min cewa garambawul din da gwamnati na tayi a fanin banki ne ya bashi damar tabbatar da dukkan nasarorin da ya samu a kasuwancinsa na bangaren siminiti," inji Obasanjo.

Obasanjo ya ce al'ummar Afirka ne za su iya kawo cigaba a nahiyar kuma ya zama dole kasashen nahiyar su fara yin abubuwa yadda suka dace.

Ya kuma ce Afirka za ta cigaba da fargabar yakin tattalin arziki da wasu nahiyoyi har sai lokacin da ta inganta kasuwanci tsakanin kasahenta da 50%.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment