Monday, 1 October 2018

Nasko ne dan takarar PDP a Naija, Zai kara da gwamna Abubakar Bello na APC

Dan takarar gwamnan jihar Neja karkashin jam’iyyar PDP, Umar Nasko ya doke Musa Ibeto, Dogonkoli, Sudan da Baka a zaben fidda gwani da aka yi a jihar.


Idan ba a manta ba Ibeto wanda shine jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu ya yi murabus da wannan kujera ne a kwanakin baya inda ya canja sheka daga APC zuwa PDP.

Bayan ya canja shekar ne, ya sayi fom din takarar gwamnan jihar.

Nasko wanda shine dan takaran jam’iyyar a 2015, ya doke dukkan abokan hamayyar nasa su hudu.

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ne ya lashe zaben fidda gwani na gwamna da aka yi a jih

‘Yan jam’iyyar ne suka yi tururuwa zuwa filin da aka gudanar da zaben a jihar inda gabadayan su suka sake zaben gwamnan jihar ya zarce karo na biyu.

Premiumtimeshausa.

No comments:

Post a Comment