Thursday, 4 October 2018

Pepsi da Coca-Cola na shirin samar da lemun wiwi

Kamfanonin Coca-Cola da Pepsi sun sanar da shirinsu na samar da wani lemun kwalba mai dauke da tabar wiwi a cikinsa saboda masu shan tabar su samu abun kwankwada.


Mahukuntan Coca-Cola da Pepsi sun ce, yanzu haka suna kan nazari sosai kafin daukan matakin karshe kan lamarin, yayin da suka nuna alamar cewa, daukan matakin ka iya tasiri wajen habbaka kasuwancinsu.

Tun kafin wannan lokaci, Kasashe da dama sun halarta amfani da wiwi musamman a Kasashen da ke yankin Amurka.

Coca-Cola ne ya fara sanar da shirinsa kafin Pepsi ya biyo bayansa.

Dr. Abdullahi Isa Kauran Mata, kwararren likita a asibitin koyarwa na mallam Aminu da ke jihar Kano a Najeriya ya ce, irin wannan lemu na tattare da illoli sosai domin kuwa illolin sun fi amfaninsa yawa.

Daga cikin illolin sun hada da haddasa cutar mantuwa da ka hana mai shan lemun na wiwi shiga fagen koya ko kuma koyar da ilimi kamar yadda Dr. Kauran Mata ya yi Karin bayani a hirarsa da RFI Hausa.

No comments:

Post a Comment