Wednesday, 3 October 2018

Rahoto akan wasannin cin kofin zakarun turai da aka buga jiya: Pogba yace an hanashi magana: Madrid sun yi abinda ba su taba yi ba tun shekaru 11 da suka gabata

A wasan da aka buga jiya na gasar cin kofin zakarun turai tsakanin Juventus da Young Boys, duk da cewa Ronaldo be buga wasan ba yana gefe yana kallo saboda jan katin da aka bashi da yayi sanadin hanashi buga wasa daya, Juve taci kwallaye 3 wanda duka Paulo Dybala yaci su.


A haka aka tashi wasan Juve na da ci 3 Young Boys na da 0.

Da yake magana bayan kammala wasan, Dybala yace, duk da babu Ronaldo gashi sun yi wasa me kyau, ya kara da cewa wasa babu Ronaldo ba abune me sauki ba amma hakanan ma dole su mayar da hankali dan yin abinda ya kamata.
Hoton Ronaldo yana kallon wasan Juventus jiya


Wasan da aka buga jiya wanda shima ya dauki hankula shine tsakanin Mancester United da Valencia sun tashi babu wanda yaci kwallo wanda hakan yasa masoyan Man U da dama da tuntuni suke hake da me horas da kungiyar, Jose Mourinho suka rika kiran da a sallameshi kawai.

Wani lamari da ya kara daukar hankali shine kyaftin din kungiyar, Antonio Valencia da bayan kammala wasan yayi likin wani rubutu da akayi na kiran a kori Mourinhon, an sokeshi akan wannan lamari, saidai daga baya ya fito ya bayar da hakuri inda yace yayi likin hoton da ya ganine ba tare da ya lura da abinda aka rubuta a jikinshi ba amma bashi da wata matsala da Mourinhon.

Shima Pogba wanda wanda ya dade yana samun rashin jituwa da Mourinho da aka tambayeshi me zai ce bayan kammala wasan ya bayyana cewa, an hanashi yin magana.

Wasa na gaba da ya dauki hankula shine  wanda aka buga tsakanin Real Madrid da  CSKA Moscow wanda aka tashi ana cin Madrid 1-0. Rabon dai da Madrid ta samu irin wannan sakamakon tun shekaru 11 da suka gabata, dan kuwa ba wannan ne wasa na farko da suka rasa ba.

Golan Madrid din, Keylor Navas yayi kewar rashin Ronaldo inda yace gaskiya dan wasan ya bar babban gurbin da har yanzu ba'a samu wanda ya iya cike shiba, Lokacin yana nan yana cin kwallaye da yawa, injishi.

Saidai yace duk da babu Ronaldon dole su ci gaba da wasa.

Sauran wasannin da akayi a jiyan sune:

Hoffenheim 1
Man. City 2

Lyon 2
Shakhtar Donetsk 2

Roma 5
Plzeƈ 0
No comments:

Post a Comment