Thursday, 4 October 2018

Rahoto akan wasannin cin kofin zakarun turai da aka yi jiya

A wasannin da aka buga na cin kofin zakarun turai jiya, Liverpool ta sha ci daya me ban haushi a hannin Napoli, Salah ya bayyana cewa gaskiya rashin kokarinsune ya ja musu rashin nasara a wasan.


The Mirror ta ruwaitoshi yana cewa basu yi kokarin samun damarmaki yanda ya kamata ba sannan golansu ne yafi kowane dan wasa kokari a wasan na jiya wanda ba haka ya kamata ba.

UEFA dai taci tarar Napoli saboda kunna wata wuta da magoya bayanta suka yi a filin wasan.

Haka ma PSG wadda ta lallasa Red Star da ruwan kwallaye 6-1 ta samu tara daga UEFA saboda iface-ifacen da magoya bayansu suka yi a filin wasan da kuma kunna wata wuta.

Sauran wasannin da aka yi jiya da sakamakon yanda suka kare sune:

Tottenham 2
Barcelona 4

PSV Eindhoven 1
Inter Milan 2

Dortmund 3
Monaco 0

Atl├ętico Madrid 3
Club Brugge 1

Lokomotiv Moscow 0
Schalke 04 1

Porto 1
Galatasaray 0

No comments:

Post a Comment