Saturday, 27 October 2018

Ronaldo ya ceci Juventus da kwallaye 2

Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo ya ciwa kungiyar tashi kwallaye biyu a lokacin da take neman nasara ido rufe a wasan da suka buga da Empoli yau, Asabar.


Empoli ce ta fara cin kwallo wanda wannan karin shine na farko da Juventus ke neman ramuwar kwallo dan yin nasara tun fara kakar wasan bana na Seria A, ana cikin mintuna 54 Ronaldo ya rama wa Juve kwallon da ake cinta da bugun Fenareti.

Sai kuma ta biyu da ya ci wadda ya zandama shot daga wajen 18  ta shiga raga.

Wannan ce kwallo ta bakwai da Ronaldon ya ciwa Juventus. An tashi wasan 2-1.

No comments:

Post a Comment