Wednesday, 31 October 2018

Ronaldo ya kafa tarihi a Juventus wanda rabon da a samu irinshi shekaru 60 kenan

Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo sanannene wajan kokarin ya kafa tarihi a duk inda ya samu kanshi yana buga kwallo, a yanzu haka ya kafa tarihin da rabon da a samu dan kwallon da yayi irin bajintar da ya nuna a Juventus tun shekaru 60 da suka gabata.


Da farko da ya fara wasa a Juventus, Ronaldo bai samu cin kwallaye ba amma tun da ya warware ya fara cin kwallaye, abin sai sam barka, ya zuwa yanzu dai ya buga wasanni 10 da kungiyar ta Juve kuma ya ci kwallaye 7.

Rabon da wani dan wasan Juve ya ci yawan wadannan kwallaye a wasa goma kacal tun kakar wasan 1957/58 wanda tsohon dan wasanta, John Charles yaci.

Shidai wancan dan wasa ya kare da ciwa Juve kwalalaye 28, abinda ake jira a gani Ronaldon zai iya kamoshi ko kumama ya wuceshi ko kuwa a'a?

Lokaci dai be bar komai ba.

No comments:

Post a Comment