Saturday, 20 October 2018

Ronaldo ya zama na farko da ya ci kwallaye 400 a gasar turai

Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin kasancewa dan kwallo na farko da ya ci jimullar kwallaye 400 a manyan gasar cin kofika 5 na nahiyar turai.


Ronaldo dai ya kasance yana hamayya da Messi akan wanene cikinsu sarki ko kuma gwani na gwanaye a harkar kwallo.

Ronaldo ya ciwa Man U kwallaye 84.

Sannan ya ciwa Real Madrid kwallaye 311

Yanzu kuwa ya ciwa Juventus kwallaye 5.

Idan aka hada gaba daya zasu bayar da yawan kwallaye 400 kenan wanda shine dan wasa na farko daya taba kai wannan mataki na yawan kwallaye.

Messi ne ke bimai baya da yawan kwallaye 389.

No comments:

Post a Comment