Tuesday, 23 October 2018

Ronaldo yaji dadin tarbar da Man U tamai

Tauraron dan kwallon kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo ya godewa tsohuwar kungiyarshi ta Manchester United bisa irin tarbar da suka mishi, a yaune dai Juventus zata kara da Man U din a ci gaba da gasar cin kofin zakarun turai.Ronaldo yace jinshi yake kamar a gida.

Badai Ronaldo bane kadai wanda zai fuskanci kalubalen haduwa da tsohuwar kungiyarshi ba.

Akwai Paul Pogba wanda shima tsohon dan wasan Juventus ne.

Wasa ne me zafi duk da yake ana baiwa Juventus kyakkyawan zaton yin nasara saboda yanda yanzu Man U din ta zama sai a hankali amma komai zai iya faruwa dan haka a kayi tsammanin Chelsea zata lallasata amma suka tashi can ja rasa.

No comments:

Post a Comment