Sunday, 21 October 2018

Rundunar sojin Najeriya ta fitar da sabuwar sanarwa

Rundunar sojin Najeriya ta fitar da sabuwar game da neman da jami'an ta ke cigaba da yi a garin Jos, jihar Filato inda ta gargadi jama'a da su guji yada jita-jita da kuma labarun karya game da ayyukan nasu.

Wannan kiran dai na cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar ta jihar Filato Kanal Kayode Ogunsonya ya fitar a ranar Asabar biyo bayan wata jita-jita da ake yadawa na cewa sojojin sun kashe wata mata a garin na Dura-Du.

A sanarwar, Kanal Kayode ya karyata maganar inda yace jami'an su ba su kashe kowa ba, hasali ma jami'an su suna nan duk sun dukufa suna yin aikin su na neman Janar din da har yanzu ba'a gani ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a farkon watan jiya ne dai Janar Alkali ya bace akan hanyar sa ta zuwa Bauchi daga garin Abuja wanda kuma bincike ya tabbatar da gano motar sa a cikin wani kududdufi a garin Dura-Du.
Legit.ng

No comments:

Post a Comment