Tuesday, 16 October 2018

Sake zabar Buhari yayi shekaru 4 a mulki matsalane dan ba shi ke gudanar da mulkinba>>Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa ba shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ke gudanar da harkar gwamnati ba, wasu ne yake wakiltawa suna mishi aiki dan haka be kamata a sake zabarshi yayi shekaru 4 akan mulki ba.

Gwamnan ya bayyana hakane a lokacin da kwamitin sulhu na jam'iyyar PDP ya kaimai ziyara a gidanshi na Maitama dake Abuja, kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa be ji haushin faduwa zaben fidda gwanin jam'iyyar da yayi ba wanda Atiku Abubakar ya lashe kuma zai bayar da dukkan gudummawar da ta dace dan ganin jam'iyyar ta kai ga nasara a zaben 2019 me zuwa.

No comments:

Post a Comment