Wednesday, 3 October 2018

Sanata Dino Melaye ya lashe zaben fidda gwanin PDP

Sanata Dino Melaiye dake wakiltar mazabar Kogi ta yamma ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar Sanatan yankin nashi karkashin jam'iyyar PDP.


Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa an dan so a samu ya mutsi amma daga baya abubuwa sun daidaita, biyu daga cikin 'yan takarar sun jayewa Sanata Dino wanda kwanakin baya ya fice daga APC zuwa tsohuwar jam'iyyar tashi ta PDP.

Haka kuma akwai 'yan takara 4 da ba'a tantancesu ba.

A sakonshi na bayan zabe, Sanata Dino ya godewa wakilan jam'iyyar da suka zabeshi sannan kuma yayi kira ga wadanda suka yi rashin nasara da su zo su hada hannu dan kawar da gwamnatin APC a jihar da ma Najeriya baki daya.

No comments:

Post a Comment