Tuesday, 23 October 2018

Sanata Kwankwaso Ya Jajantawa Al'ummar Jihar Kaduna

Sanatan Kano Ta Tsakiya kuma tsohon Gwamnan jihar Kano Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ya jajantawa al'ummar jihar Kaduna bisa barkewar rikicin da aka samu a wasu sassan jihar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da asarar dukiyoyi.

Sanatan wanda ya bayyana hakan ta bakin Hadiminsa, Shehu M. Bello (Shehun Garu), ya yi addu'ar Allah ya kiyaye aukuwar hakan a fadin kasar nan baki daya a nan gaba.
Rariya.

No comments:

Post a Comment