Saturday, 6 October 2018

Sanata Shehu Sani ya fice daga zaben fidda gwanin Kaduna

Me taimakawa sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ta bangaren watsa labarai, Abdulsamad Amadi ya fitar da sanarwa inda ya bayyana cewa Sanata Shehu Sani ba zai shiga zaben fidda gwanin takarar Kaduna ta tsakiya na APC da ake yi a jihar ba.


Shehu Sani ya bayyana zaben a matsayin haramtacce inda yace uwar jam'iyya shi kadai ta sani a matsayin dan takara dan haka babu wani zabe da zai je ayi dashi kuma babu wani wakili da zai tura, duk ma wanda yaje da sunanshi to bashi ya turashi ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sani ya kara da cewa shi dan kasa na garine me bin dokar kasa da ta jam'iyya.

No comments:

Post a Comment