Thursday, 25 October 2018

Sanata Shehu Sani ya sake baiwa wani abokin aikinshi shawara a fakaice

A dazu ne muka ji cewa sanata Shehu Sani me wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai ya baiwa abokin aikinshi, Ike Ekweremadu shawarar kada ya koma APC idan kuma bai ji bari ba to ya ji hoho, da alama dai Shehu Sanin ya kara baiwa wani abokin aikin nashi shawara.


Saidai a wannan karin yayi amfani da sunan Timi ne kawai inda yace, dan uwa Timi, ka yi kokari ka bar wannan gurin, kada wuya ta kashe ka. Sun fa ji barazanar da kayi amma babu abinda zai faru, kawai ka hau jirgi me zuwa ka tafi gida.

No comments:

Post a Comment