Tuesday, 2 October 2018

Sanata Shehu Sani Ya Samu Tikitin Sake Tsayawa Takara

Rahotanni daga Kaduna sun nuna cewa dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani bayan ya fafata da Ibrahim Usman (Sardauna Badarawa); Shamsu Shehu Giwa; Janar. Mohammed Sani Saleh da kuma mai ba Gwamnan kaduna shawara kan Harkokin siyasa, Uba Sani, Dubban Jama'a magoya bayan Jam'iyyar APC a Jihar Kaduna, sun gudanar da wata gagarumar tarzoma ta kin amincewa da ayyana sunan Sanata Shehu Sani a matsayin halastaccen Dan takara na Jam'iyyar APC wanda zai tsaya takarar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a zaben 2019.

Dubban 'ya'yan APC din wanda suka yi dafifi zuwa Sakatariyar jam'iyyar da ke titin Ali Akilu a garin Kaduna, sun nuna damuwa gami da Allah wadai akan matakan da uwar Jam'iyyar ta kasa ta dauka karkashin jagorancin Shugaban Jam'iyyar Adams Oshiomole inda aka bayyana sunan Shehu Sani a matsayin Dan takara, sannan suka jadadda goyon bayan su ga Alhaji Uba Sani, wanda shima ya fito takara ta Sanata mai wakiltan yankin. 

Mai magana da yawun 'ya'yan APC din Sa'idu Dilbis ya ce sun yi bakin ciki sosai da abinda APC ta kasa tayi, kuma lallai suna kira da babbar murya da uwar Jam'iyyar ta gaggauta janye wannan mataki da ta dauka sannan su baiwa jama'a wanda suke so ya wakilce su, wanda zabin jama'ar Kaduna ta tsakiya shine Uba Sani inji su.
Rariya.

No comments:

Post a Comment