Tuesday, 2 October 2018

Sanatan da ya bar APC zuwa PDP dan yin takarar gwamna ya sha kasa

Sanata Suleiman Othman Hunkuyi da irin su tsohon Shugaban NEMA sun fadi zaben fitar da gwani na takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar PDP a hannun Isah Ashiru Kudan.

Sanatan na Arewacin Jihar Kaduna ya sha kasa ne a zaben da aka gudanar a karshen makon nan inda ya zo na biyu. Suleiman Hunkuyi ya samu kuri’u 564 yayin da Malam Muhammad Sani-Sidi ya tashi da kuri’a 560 a zaben.

Tsohon Sanatan na Jam’iyar APC yayi biyu-babu dai yanzu a Jihar Kaduna bayan bai samu tikitin PDP a zaben ba. Sanatan dai ya bar APC ne zuwa PDP kwanaki domin yayi takarar kujerar Gwamna mai-ci da Nasir El-Rufai.

Alhaji Isah Ashiru wanda tsohon ‘Dan Majalisar Wakilan Tarayya ne yayi nasara a zaben fitar da gwanin da aka yi inda ya samu kuri’u 1330. Tsohon Gwamnan Kaduna Mukhtar Ramalan-Yero yana cikin wanda ya sha kashi a zaben.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment