Tuesday, 9 October 2018

Sanatocin APC sun yi taro kan tsige Bukola Saraki

Wasu sanatocin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya sun gudanar da taron gaggawa a cikin daren da ya gabata game da makomar shugaban Majalisar Dattawan Kasar, Bukola Saraki.


Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Sanatocin sun gana ne a birnin Abuja don tattaunawa kan yadda za su tsige Saraki daga mukaminsa na shugaban majalisa bayan sauya shekarsa daga APC zuwa babbar jam'iyyar PDP mai adawa.

Ko da yake wasu rahotannin na cewa, Sanatocin sun tafka zazzafar muhawara kan batun tsigewar, in da wasu ke cewa, jam’iyyar ta APC ba ta yi musu adalci kan wasu batutuwa.

Da ma tun bayan ficewar Saraki daga APC zuwa PDP, Sanatocin APC suka lashi takobin tsige shi da mukaminsa, in da suke cewa, dole ne jam’iyya mai mulki ta rike kujerar shugaban majalisa saboda rinjayenta a majalisar.

Wannan na zuwa ne a yayin da Majalisar Tarayyar Kasar ke komawa bakin aiki a ranar Talata bayan shafe fiye da watanni biyu na hutu.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment