Sunday, 7 October 2018

Sani Danja a gurin zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na PDP>>Ni da Me gidana Jonathan

Tauraron fina-finan Hausa da turanci kuma mawaki, Sani Musa Danja, Zaki kenan a wadannan hotunan inda ya halarci taron zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar Rivers.Danja ya bayyana cewa ina tare da me gidana, Goodluck Jonathan gwarzon dimokradiyya shugaba na farko a Duniya da yana kan mulki ya taya abokin hamayyarshi murnar cin zabe tun kamin a bayyana sakamako a hukumance.

An kuma ga Sani Danja da kakakin majalisar Dattijai, Yakubu Dogara.


No comments:

Post a Comment