Tuesday, 2 October 2018

Saraki ya bayyana dalilin da yasa be halarci bikin ranar 'yanci a Eagle Square ba

A jiya, Litinin aka yi shagalin tunawa da ranar samun 'yancin kan Najeriya daga turawan mulkin mallaka inda shugaban kasa, Muhammadu Buhari da mataimakinshi, Farfesa Yemi Osinbajo da tsaffin shuwagabannin kasa, Yakubu Gowon da Abdulsalam Abubakar dadai sauransu suka hadu a filin Eagle Square dake babban birnin tarayya, Abuja, sojoji suka yi fareti.


Saidai wani abu da ya dauki hankula a gurin taron shine rashin zuwan shuwagabannin majalisar tarayya, Bukola Saraki da Yakubu Dogara gurin wannan taro. Hakan ya kara fito fili da rashin jituwar dake tsakanin bangaren zartarwa da na dokoki.

Bukola Saraki ta hannun me magana da yawunshi, Yusuph Olaniyonu ya bayya dalilin da yasa be halarci wannan guri ba, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

Ya bayyana cewa, yana da wasu muhimman taruka da ya kamata ya halartane sannan kuma a jiyanne aka yi zaben fidda gwanin da zai tsaya takarar gwamna karkashin jam'iyyar PDP a jihar shi ta Kwara wanda yana bukatar ace yana gurin.

Bugu da kari a jiyanne dai ya kuma gana da Delegates na jihar Kogi a kokarin samun tikitin tsayawa takarar shugaban kasa da yake yi karkashin tutar PDP, wadannan sune dalilan da yasa be halarci Eagle Square ba.

Ta bangaren kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara kuwa, me magana da yawunshi, Turaki Hassan ya bayyana cewa, baya Abuja dan haka bai san abinda ke gudana a can ba, sannan bashi da masaniyar ko an gayyaci me gidan nashi taron ba.

No comments:

Post a Comment