Saturday, 13 October 2018

Sheikh Gumi ya bayyana dalilin da yasa ya je gamawar Atiku da Obasanjo

Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, daya daga cikin malaman addinan da suka shaida sasantawar tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar PDP a zaben 2019 wato Atiku Abubakar da kuma tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, ya yi karin haske a game da sasantawar da suka halarta.


Sheikh Gumi, ya shaida wa BBC cewa, shi dai an gayyace shi ne domin ya zama shaida a sulhun da aka yi tsakanin Atiku Abubakar da kuma Obasanjo.

Malamin addinin Islaman, ya ce an zabe su su je sulhun ne saboda ana neman mutanen da ba ruwansu da bangaranci addini kawai suka sanya gaba, shi ya sa yakasance daya daga cikin masu sulhun.

Sheikh Gumi ya ce, sun zama shaida a sulhun da aka yi ne, bisa la'akari da cewa duk wani abu da zai kawo sulhu a addinin musulunci, abu ne wanda aka kwadaitar da shi a yi shi.

Malamin addinin Islaman, ya kuma yi karin haske a kan zargin da ake cewa ko suna nuna goyon bayansu ne ga takarar Atiku Abubakar, inda ya ce ' Ba a Atiku Abubakar ba, ko wanene koda a misali shugaba Muhammadu Buhari zai fito ya ce zai yi sulhu da kanal sambo Dasuki da aka kulle, a nemi ni a ce na zo nayi sulhi, to zan yi'.

Sheikh Gumi ya kuma bayyana irin alfanun da ya ke ganin wannan sulhu na su Atiku da Obasanjo zai yi, inda ya ce abu na farko akwai rikici a kasar nan, yawanci kowa a cikin manyan kasar na ganin an cuce shi,to a irin hakan an bukatar yafiya don shi kasa ke bukata.

Malamin addinin ya ce, shi fa a bangarensa ba ya goyon kowa a takarar shugabancin kasa, domin ko iyalansa ma ba zai ce musu ga wanda za su zaba ba, don haka shi ba shi da zabi, kuma kowa na da na sa zabin.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment