Friday, 12 October 2018

Shekaru 5 kenan ina daukar nauyin karatun yara mata da rikicin Boko Haram ya kora daga gidajensu

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa shekaru biyar kenan yana daukar nauyin karatun yara mata da suka rasa gidajensu sanadiyyar fadan Boko Haram.


Atiku ya bayyana hakane a dandalinshi na sada zumunta a matsayin sakon ranar yara mata ta Duniya, ya kuma yi kira da a rika kokarin baiwa yara mata ilimi.

No comments:

Post a Comment