Sunday, 21 October 2018

Shin APC Ta Yaudari Sanata Shehu Sani Ne?

A jiya ne Sanatan da ke wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya ayyana ficewa daga cikin uwar jam’iyyar APC, lamarin na zuwa ne biyo bayan wasa da hankalinsa da shigo-shigo da uwar jam’iyyar ta masa inda daga bisani ta ki tsaida shi a matsayin dan takararta na Sanata.


Tun da fari dai Sanata Shehu Sani an yi ta samun bayanai da suke cewa jam’iyyar ta tsaida shi a matsayin dan takararta guda, sai a lokacin mika sunaye ga hukumar zabe ta kasa INEC kawai sai APC ta sauya da sunan wani ba shi ba.

A wani wasikar da Sanata Sani, ya aike wa gundunarsa, ya shaida musu cewar ya fice daga jam’iyyar.

A wani hirarsa da manema labaru Sanata Shehu ya shaida cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sake gwamnonin APC sun fi karfinsa.

Ya shaida cewar talakawa da al’umman Nijeriya suna son jam’iyyar ne a sakamakon manufofi da ka’idojin da jam’iyyar ta sanya a gaba, inda ya yi zargin cewar wasu gwamnonin da suke jam’iyyar sun dauko hanyar ruguza wannan kaunar da talakawa ke yi wa jam’iyyar a bisa tafka rashin adalci da rashin kan gado a hidimar jam’iyyar.

Sai dai kuma duk da cewa Sanatan bai samu tikitin sake takarar kujerar mazabar tasa ba a karkashin APC, ya tabbatar da cewa tabbas zai yi takarar domin akwai jam’iyyun da suka riga suka tsayar da shi amma bai bayyana su ba, idan lokaci ya yi zai sanar.

Shehu Sani ya alakanta ficewar tasa da yadda aka gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar a jihohi ta yadda sai abin da gwamnoni suka zaba ba jama’a ba shi ne uwar jam’iyyar ma a tarayya za ta amince da shi.

Sanatan ya ce tun a baya ya yi yunkurin ficewa daga jam’iyyar lokacin sauran takwarorinsa ‘yan majalisu suna ficewa, amma uwar jam’iyyar ta dakatar da shi bisa alkawarin cewa za a daidaita al’amura, amma kuma a yanzu alkawarin ya zama kamar yaudara.

Dan majalisar dattawan yana da takaddama da reshen jam’iyyar na jiharsa wanda ke bin bayan gwamnatin jihar a game da tikitinsa na sake yin takarar kujerar a zaben 2019, inda jam’iyyar ta mika sunan mai ba wa gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufa’i shawara kan harkokin siyasa Malam Uba Sani a matsayin dan takarartar da ta tsayar.

Kafin hakan hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja tun a baya ta sanar da cewa Shehu Sani shi kadai ne aka wanke da zai yi takarar kujerar, matakin da gwamnatin jihar da reshen jam’iyyar na jihar suka ki amincewa, a gefe guda kuma jama’a na kallon wannan lamarin amatsayin tarkon da aka dana wa Sanata Sani kana ya gaza gano inda daga bisani suka rufta da shi ta hanyar tsaida wani bashi din ba.

Sanata Shehu Sani da gwamna El-Rufa’i daman kusan ba sa ga-maciji da juna tun bayan zabensu a shekara ta 2015, duk da cewa ‘yan jam’iyya daya ne, ta yadda ma har sukan yi amfani da kalamai na batanci ga junansu.
Leadershiphausa.


No comments:

Post a Comment