Friday, 12 October 2018

Shin tabarrakin Obasanjo zai iya ba Atiku nasara a 2019?

Tun bayan da tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ake ta tafka muhawwara a ciki da wajen kasar.


Ko da ya ke wasu na ganin hakan ba zai yi wani tasiri ba, amma wasu kuma na ganin hadin gwiwar manyan 'yan siyasar Najeriyar biyu wani babban kalubale ne ga Shugaba Muhammadu Buhari wanda ke neman wa'adin mulki na biyu.

Atiku Abubakar dai shi ne mataimakin shugaban Najeriya daga 1999 zuwa 2007 lokacin Obasanjo kuma na shugaban kasa, amma daga bisani suka raba gari, inda tsohon shugaban kasar ya yi ta sukar tsohon mataimakin nasa tare da cewa ba zai taba goya masa baya ba.

To amma ga alama sun dan sulhunta.

Bayan da ta bayyana cewa Atiku Abubakar ya kasance dan takarar jam'iyyar PDP, ga alama Obasanjo ya shiga yanayi na gaba kura baya sayaki kan mutumin da ya kamata ya mara wa baya a zaben da ke tafe.

Shin ya goyi bayan Aitku wanda a baya ya sha alwashin ba zai goyi bayansa ba?
Ko kuwa ya goyi bayan Shugaba Buhari - mutumin da a cikin wannan shekarar ya soki salon shugabansa da kuma ba shi shawara cewa ya yi murabus saboda rashin iya shugabanci?

Bisa dukkan alamu Obasanjo na ganin Atiku ya fi dama-dama a gare shi.

A cikin watannin baya dai, Shugaba Buhari ya nuna alamar gwamnatinsa za ta bincike tsohon Shugaba Obasanjo musamman kan kudi dalar Amurka biliyan 16 da aka kebe domin samar da wutar lantarki a zamanin mulkin tsohon shugaban.

To amma mutane da dama na ganin Cif Obasanjo ba kashin yarwa ba ne a siyasar Najeriya - yana da tasiri sosai.

Tun bayan da ya sauka daga karagar mulki a 2007 ya ci gaba da sukar duk gwamnatin da ta gabace shi.

Wani abin lura kuma shi ne, tun daga lokacin duk dan takarar shugabancin kasa da Obasanjo ya mara wa baya yakan samu nasarar zama shugaban kasa - tun daga marigayi Alhaji Umaru Musa Yar'Adua a 2007 zuwa ga Dr Goodluck Jonathan a 2011.

Kuma shi kansa shugaba mai ci yanzu Muhammadu Buhari a 2015 ya samu goyon bayan Obasanjon a baya.

Sai dai Shugaba Buhari da mukarrabansa na cewa suna da kwarin gwiwar cewa duk da yadda wadansu suka sauya sheka daga jam'iyyarsa.

Kuma wasu manya a kasar ke juya masa baya, shugaban na da goyon bayan talakawan kasar musamman a arewaci da yankin kudu maso yammacin kasar.

Haka kuma wata sanarwa ta mai magana da yawun Shugaba Buhari Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce hadewar Obasanjo da Atiku wani kawance ne na rungume ni mu fadi, domin dukkanninsu biyu za su sha kaye.

To amma a lokacin da Atiku Abubakar ya kai masa ziyara a ranar Alhamis a gidansa da ke Abeokuta, tsohon Shugaba Obasanjo ya bayyana shi a matsayin 'shugaban kasa da ke tafe', sannan ya yaba da abin da ya kira 'gogewa' ta Atiku.

Shugaba Buhari yana takarar ne karkashin jam'iyyar APC, yayin da Atiku Abubakar yake takara a babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

A karshen makon jiya ne duka jam'iyyun suka kammala zabukan fitar da gwani.

Kuma akwai yiwuwar ci gaba da samun sauye-sauye da kuma karin kawancen siyasa a gabanin zabukan da aka shirya gudanarwa a watan Faburairun 2019 - don haka ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment