Wednesday, 24 October 2018

Shugaba Buhari da Patrice Talon na Benin sun kaddamar da sabuwar mashiga dake tsakanin kasashen

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan tare da shugaban kasar Benin Republic, Patrice Talon a gurin kaddamar da sabuwar mashigar da aka gina da ta hade iyakar Najeriya da Benin din.


Akwai gwamnan Legas, Ambode da sauran wasu manyan jami'an gwamnati a gurin wannan bii da ya faru jiya, Talata.

Da yake jawabi a gurin taron shugaban Buhari ya bayyana godiyar shi da jin dadi da gina wannan mashiga inda yace zata habbaka harkar kasuwanci da kuma saukaka zirga-zirga tsakanin kasashen dake yammacin Afrika ya godewa Kungiyar ECOWAS da EU da kasar ta Benin bisa wannan namijin kokari.


No comments:

Post a Comment