Saturday, 20 October 2018

Shugaba Buhari na son haduwa da yaron da ya mai wannan zanen

Wani me suna Jide ya bayyana cewa wani yaron makwaucinshi dan shekaru 11 ya tinkareshi da wannan zanen da ya yiwa shugaba Buhari ya rokeshi akan ya sakashi a yanar gizo.Ai kuwa sai akai gam da katar hoton ya kai idon Bashir Ahmad, me taimakawa shugaba kasa kan sabbin kafafen sadarwa, ya kuma tabbatar da cewa, Shugaba Buhari ya ga hoton ya kuma kayatar dashi harma yana son haduwa da yaron.

No comments:

Post a Comment