Thursday, 25 October 2018

Shugaba Buhari, Wike, da ministoci a gurin bude gurin hada-hadar fasinja na filin jirgin saman Fatakwal

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan tare da gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike da ministan sufurin jirgin sama, Hadi Sirika da Ministan kwadago, Chris Ngige a jihar ta Rivers inda ya bude gurin hada-hadar fasinja na filin jirgin sama na kasa da kasa dake jihar.


A gurin taron shugaba Buhari ya bayyana cewa, wannan aiki zai amfani fasinja dake shigowa daga kasashen waje zuwa kudancin kasarnan dama Najeriyar baki daya, kuma gwamnatinshi zata ci gaba da inganta rayuwar jama'a da irin wannan ayyuka da kuma harkar noma.

Shugaba Buhari yace, Najeriya ta samu dama lokacin da mai yayi tsada a Duniya amma sai wasu tsiraru masu son kai da handama suka amfanar da kansu da wancan arziki maimankon a wa kasa aiki. Ya bayyana cewa wannan abu ya kare.

No comments:

Post a Comment