Friday, 26 October 2018

Shugaba Buhari ya bayyana aiki mafi muhimmanci da Amurka da Turai zasu wa Afrika

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amshi bakuncin ma'aikatar kungiyar hadun kan Afrika, Moussa Faki Mahamat a fadarshi ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja, a lokacin ganawar tasu shugaba Buhari ya bayyana baban hannun jarin da kasashen Amerika da Turai zasu zuba a Afrika.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa aikin dawo da ruwan tafkin Chadi dake shirin kafewa shine babban aikin da kasashen Amerika da Turai zasu wa Afrika a yanzu, yace a yanzu ruwan ya koma kashi 10 kawai cikin 100 na yanda aka sanshi a baya Saboda dumamar yanayi.

Kuma hakan ya taimaka wajan rasa aikin mutane da dama da suka fito daga kasashen Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru masu sana'o'in masunta, makiyaya da manoma sun rasa ayyukansu wanda hakan na daga abinda yake taimakawa wajan tafiyar matasa kasashen turai da Amurkar ci rani.

Yace dawo da ruwan zai taimaka wajan rage tafiya ci rani da matasa ke yi zuwa kasashen turai. Ya kuma tabbatar da cewa Najeriya zata ci gaba da bayar da gudummuwarta wajan ci gaban Afrika.

A nashi jawabin, Mahamat ya yabawa shugabancin Shugaba Buhari inda yace abin koyi ne ga sauran shuwagabannin Afrika, kamar yanda sanarwar me magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ta bayyana.

No comments:

Post a Comment