Friday, 12 October 2018

Shugaba Buhari ya gana da musulmin basaraken Inyamurai

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan a wadannan hotunan lokacin da yake amsar bakuncin basaraken, Umuofor Eze Abdulfatah Emetumah daga jihar Imo wanda kuma shine shugaban limaman karamar hukumar, Oguta da ya fito.A lokacin ganawar tasu, shugaba Buhari ya tabbatar musu da cewa babban abinda yasa ya zama shugaban kasa shine dan ya inganta rayuwar 'yan Najeriya, kuma duk wanda yayi wargin kawo rabuwar kasarnan, matukar suna raye to ba zasu barshi ba.

No comments:

Post a Comment