Thursday, 4 October 2018

Shugaba Buhari ya gana da tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu: Karanta abinda yace mai akan yaki da cin hanci

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amshi bankuncin tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Thabo Mbeki yau a fadarshi ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja, Mbeki ya jagoranci wata tawagar kungiyar hadin kan Afrika, AU ce zuwa Najeriya.


Da yake jawabi a lokacin ganawar da suka yi, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa Yaki da rashawa da cin hanci ba abune wanda ya daukeshi da sauki ba saboda akan shine aka zabeshi kuma alkawuran da suka yi shine yaki da cin hanci da tsaro da kuma habbaka tattalin arziki, kamar yanda yake a wata sanarwar bayan taro da me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar.
No comments:

Post a Comment