Tuesday, 30 October 2018

Shugaba Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Kaduna

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Kaduna da ke arewacin kasar wacce ke fama da rikici.


Gwamnan jihar Nasir el-Rufa'i ya tarbi Shugaba Buhari a filin jiragen sojin saman kasar da ke Kaduna ranar Talata da safe.

Shugaban na Najeriya ya gana da sarakuna da malaman addinai da kuma shugabanninn al'umar da rikicin jihar ya shafa.

Da yake jawabi, Shugaba Buhari ya bayyana matukar rashin jin dadinsa game da rikicin da aka yi a jihar.

Ya yi jaje ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu, musamman ga iyalan Agom Adara, wanda masu satar mutane domin karbar kudin fansa suka kashe.

"Gwamnatin tarayya tana yaba wa gwamnatin jihar Kaduna bisa kokarin da ta yi na daukar matakin magance rikicin.

Muna aikewa da karin dakarun tsaro daga gwamnatin tarayya, kamar yadda gwamnatin Kaduna ta bukata, da zummar tabbatar da zaman lafiya," in ji Shugaba Buhari.
BBChausa.

Shugaba Buhari ya kuma ce gwamnatin tarayya zata tabbatar an hukunta wanda suka yi sanadin rikicin inda yace idan a da sun yi sunsha to wannan karin za'a hukuntasu.


No comments:

Post a Comment