Sunday, 7 October 2018

Shugaba Buhari ya lashe zaben fidda gwani na APC da kuri'u sama da miliyan 14:Yace 'yan Najeriya su tambayi PDP me ta yi da kudin da ta samu a lokacin mulkinta

Bayan kammala zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyya me mulki ta APC shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda dama shine dan takara daya tilo na jam'iyyar ya lashe zaben da kuri'u sama da miliyan 14.


Da yake jawabin bayan zabe, shugaba Buhari yayi godiya ga jam'iyyar da ta yadda dashi ta bashi takarar shugaban kasar ta inda yayi alkawarin ba zai basu kunya ba.

Shugaban ya kuma godewa 'yan jam'iyyar wanda suna da so da damar fitowa kuma sun cancanta da takarar shugaban kasar amma suka bar mishi saboda hadin kai da ci gaba.

Shugaban yayi bayanin cewa sun fa kawo canjin da suka yi alkawarin kawowa a kasarnan, inda ya bayar da misali da manoman shinkafa wanda a da sun cire tsammani amma yanzu sun samu tallafi daga gwamnati, da yawansu sun zama miloniyoyi.

Ya kara da cewa yanzu Najeriya na samar da kashi 80 cikin 100 na shinkafar da take amfani da ita.
Buhari ya kuma ce yanzu haka suna kokarin kafa na'urori a jami'o'in gwamnatin tarayya 9 na kasarnan dan samar da tashoshin bayar da wutar lantarki masu zaman kansu wanda zasu tabbatar da tsayuwar wutar na awanni 24, kuma nan gaba aikin zai kara fadada zuwa jami'o'i sama da 30 dake kasarnan.

Ya kara da cewa, wadanda suka yi satar kudaden gwamnati yanzu suna ji a jikinsu domin kuwa shari'a na ta maganinsu.

A karshe shugaban ya ce 'yan Najeriya su tambayi PDP wai me ta yi da kudin da ta samu daga shekarun 1999 zuwa 2015?.


No comments:

Post a Comment