Saturday, 6 October 2018

Shugaban 'yansandan kasa da kasa, Interpol yayi batan dabo

Rundunar ‘Yan Sandan Faransa ta kaddamar da bincike game da bacewar shugaban Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasa, wato Interpol, Meng Hongwei, wanda shi ne mutun na farko daga kasar China da ya rike wannan mukami.


Wata kwakkwarar majiya ta ce, an yi wa Meng ganin karshe a makon jiya bayan fitowarsa daga Shalkwatan Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasa da ke birnin Lyon na Faransa da zummar balaguro zuwa kasarsa ta asali wato Sin.

Matar Meng ce ta fara sanar da labarin bacewar maigidanta, yayin da wata majiya ta shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, ba a cikin kasar Faransa ya bace ba.

Gabanin nada shi a matsayin shugaban Interpol a shekarar 2016, Meng ya rike mukamin mataimakin Minista Tsaron Al’umma a China.

Mahukuntan birnin Beijing na ganin zaben Meng akan mukamin na shugaban Interpol a matsayin wata dama ta samun karin taimakon kasa da kasa wajen murkushe masu yi wa tattalin arzikin China zagon kasa da suka hada da manyan jami’an gwamnati da shugaba Xi Jinping ke fafutukar yakar su saboda cin hanci da rashawa.

Ana saran wa’adin Meng a kan kujerar shugabancin Interpol ya kare a shekarar 2020.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment