Thursday, 4 October 2018

Soji sun kama mutane 30 kan mutuwar Majo Idris Alkali

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kame wasu mutane 30, a jihar Filato sakamakon kaddamar da binciken da tayi kan mutuwar tsohon hafsanta Janar Idris Alkali, wanda aka gano motarsa a wani kududdufi dake yankin ‘Du’.


Karo na farko kenan da rundunar sojin Najeriyar ta yi kame, tun bayan kaddamar da bincike domin zakulo masu hannu wajen tayarda zaune tsaye, a jihar ta Filato, musamman a yankin na ‘Du’ dake karamar hukumar Jos ta Kudu.

Daga cikin abubuwa da sojin suka gano tattare da mutanen da ake zargi, akwai, bindigogi kirar gida guda shida, manya da kanana, sai kuma wukake da adduna.

Sauran kayayyakin sun hada takalman soji, katunan shiadar jami’an Vigilante 3, baburan hawa 5, da kuma babur mai kafa 3 daya.

Kamen da sojin na Najeriya suka yi, ya zo ne bayan sanar da gano wasu karin motoci hudu a cikin tafkin da ake bincike akai, domin gano gawar tsohon Janar Idris Alkali da ake zaton wasu ‘yan bindiga sun hallaka shi a ‘Doi Du’ dake karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

Babban hafsan dake jagorancin aikin binciken, Manjo Janar Augustine Agundo yace ba za suyi kasa a gwuiwa ba wajen cigaba da gudanar da ayyukan su har sai sun cimma nasara.
Gudanar da wannan bincike ya biyo bayan zargin hallaka Janar Idris Alkali, tsohon babban hafsan sojin Najeriya, da ake zargin wasu ‘yan ta’adda da aikatawa a yankin na ‘Doi Du’.

Yayin gabatar da nasarar da suka samu, Janar Agustine Agundu, yace yanzu haka sun ciro motoci guda 3 da kuma wasu tarin kayayyaki na bam mamaki.

Kwamandan runduna ta 3 na sojin Najeriya dake da Cibiya a birnin Jos, Manjo Janar Benson Akinruluyo yace zasu cigaba da aikin su har sai sun ga abinda ya turewa buzu nadi.

A wata hira da yayi da manema labarai a baya, Gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong ya sha alwashin daukar mataki mai tsauri kan masu tare hanya suna kashe mutane a Jihar.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment