Tuesday, 16 October 2018

SOJOJI SUN GANO HOTUNAN WADANDA SUKA HALLAKA JANAR IDRIS ALKALI

Kwamandan rundinar sojin Nijeriya shiyya ta uku "General Officer Commanding (GOC) 3 Army Division Rukuba Plateau State Manjo Janar Benson Akinroluyu ya karbi bakwancin babban zababben sakataren hukumar kare hakkin bil'adama ta Kasa Mr. Anthony Ojukwu, suka tafi garin Dura-Du har zuwa bakin kududdufin da aka samu motar Janar Idris Alkali 


A gurin ne Janar Benson ya fadawa sakataren hukumar kare hakkin bil'adama na kasa cewa a binciken da suke yi sun samu hotunan wadanda suke da alhakin hallaka Janar Idris Alkali, yanzu kokarin da suke yi shine su samo gawar Janar Idris domin a yi masa jana'iza da karramawa irin na sojoji, kwamandan sojojin ya kara da cewa ba zasu taba wanda bashi da alhakki a salwantar da rayuwar Janar Idris Alkali ba, don haka mutanen garin Dura-Du kada su ji tsoro, su dena yin hijira suna barin gidajensu

Sakataren hukumar kare hakkin bil'adama Mr Ojukwu ya gabatar da nasa jawabin, inda yace ya yaba da binciken da sojoji sukeyi domin basu take hakkin bil'adama ba, sannan yace su cigaba da aikin gudanar da bincike har sai sun bankado wadanda suke dauke da alhakkin salwantar da rayuwan Janar Idris Alkali 

Abinda nake nazari a kai shine zaiyi wahala ace mutanen da suka hallaka Janar Idris Alkali sun jefa gawarsa a cikin kududdufi, abin tsoron shine ta iya kasancewa sun dafa namansa sun cinye tunda dama suna cin naman mutane, ko kuma sun bunne gawarsa a cikin jeji, dayan biyun nan zai iya faruwa.

Tun da dai har an samu motarshi musamman da rigar shi, to ya kamata ace gawarsa ma tana tare da motar ko rigar jikinsa da aka kwabe, amma kunsan tsageru 'yan ta'adda suna da nasu wayon don su tsallakewa tarkon jami'an tsaro

Muna rokon Allah Ya kyautata makomar Janar Idris Alkali.
Datti Assalafy.

No comments:

Post a Comment