Sunday, 28 October 2018

Suarez ya karya tarihin da Messi da Ronaldo suka kafa shekaru 10 da suka gabata bayan da Barca ta yi raga-raga da Madrid da ci 5-1

A wasan da aka buga na Elclasico tsakanin Real Madrid da Barcelona yau, Lahadi, Barca ta lallasa Madrid da ci 5-1, an buga wasan babu shahararrun 'yan kwallon kungiyoyin biyu, Cristiano Ronaldo da Lionel Messi, saidai Suarez ya goge tarihin da 'yan wasan suka kafa kusan shekaru 10 da suka gabata.


A shekaru 10 da suka gabata a tarihin wasan Elclasico babu wanda ya taba cin kwallon bugun daga kai sai gola in banda Ronaldo da Messi, kamin su kuma Ruud Van Nistelrooy ne ya ci irinta a shekarar 2008 sai kuma ita Barca Ronaldinhone ya ci mata ta karshe, kamin Messi ya fara ci a shekarar 2006.

Suarez ne da kanshi ya samo bugun bayan da Varane ya dokeshi a 18 din Madrid kuma ya buga ya cita. Kwallaye uku yaci a wasan na yau wanda hakan yasa ya kara kafa wani tarihin kasancewa na 25 da yaci kwallaye 3 a wasan Elclasico.

Cotinho da Vidal ne suka ci wa Barca sauran kwallayen sai kuma Marcelo da ya ciwa Madrid kwallo daya wanda a haka aka tashi wasan 5-1.

Bayan wasan tuni aka fara tunanin makomar me horas da kungiyar Madrid din, Julen Lopetegui inda ake tunanin kungiyar zata koreshi, daya daga cikin wanda suka bayyana haka hadda tsohon me horas wa na Chelsea, Antonio Conte wanda ana tsammanin yana daya daga cikin wanda zasu maye Julen din idan Madrid ta koreshi

No comments:

Post a Comment