Saturday, 6 October 2018

Sun barmu ba abinci: Yunwa zata kashe mu>>Wakila PDP dake gurin zaben fidda gwani

Rahotannin dake fitowa daga jihar Rivers inda za'a yi zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyar PDP na cewa wakilan da zasu yi zaben na can suna ta lahailahaitu babu koda ruwan sha ballantana abinci.


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu daga cikin wakilan PDP sun shaida mata cewa an kawo ruwa a gurin amma ba kowane ya samu ba gashi kuma an jibga jami'an tsaro ta yanda ba sa iya yin walwala yanda ya kamata.

Wasu daga cikin wakilan sun shaidawa Daily Trust cewa suna shakkar karfa ana cikin zaben wasu su rika faduwa saboda yunwa.

Saidai jaridar tace a lokacin da take hada rahoto taga wata mota wadda ake kyautata zaton abinci ne a cikinta a farfajiyar da ake gudanar da taron amma ba'a fara rabawa ba.

Haka kuma ba'a fara zaben akan lokaci ba kamar yanda aka tsara saboda jiga-jigan jam'iyyar suna can suna wata muhimmiyar tattaunawa a tsakaninsu.

No comments:

Post a Comment