Friday, 26 October 2018

Super Eagles ta dawo ta 3 wajen iya kwallo a Afrika


Kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles ta matsa gaba da mataki 4 a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya ke fitarwa duk wata kan kasashen da suka fi iya kwallo inda yanzu ta koma ta 44.Cikin jadawalin da hukumar ta wallafa a shafinta yau Alhamis ya nuna cewa yanzu Najeriya na da maki 1431 a wanann watan fiye da na watan Satumba wanda ta ke da maki 1415.

Jadawalin na FIFA dai ya nuna cewa yanzu Najeriya ita ce kasa ta uku mafi iya kwallo a nahiyar Afrika bayan kasashen Tunusia da Senegal.

Ana dai ganin wanda dagawa da Super Eagles ta yi cikin sauri na da nasaba da nasararta kan Libya da ci 4 da banza a gida da kuma ci 3 da 2 a waje, yayin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Afrika.

Yanzu haka dai Tunisa ita ke matsayin ta 22 a Duniya sai Senegal a matsayin ta 24, yayinda kasashen Jamhuriyar Demokradoyyar Congo da Morocco ke matsayin na 46 da 47 cikin kasashe 50 mafiya iya kwallo a Afrika.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment