Friday, 5 October 2018

Ta tonu: Takardun tarukan sirri da 'yan kabilar Birom suka yi kan musulmai sun bulla a yanar gizo

Wasu takardaun tarukan sirri da bamu kai ga tabbatar da sahihancin su na zaman taron da 'yan kabilar Birom dake a jihar Filato suka gudanar akan musulmai da 'yan kabilar Hausawa, fulani, Inyamurai da dai sauran su sun bulla a saman yanar gizo.


Takardun na zaman wanda aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuni na shekarar 2010 mun samu cewa ya samu halartar mutane da dama 'yan asalin kabilar ta Birom ciki hadda gwamnan jihar a wancan lokacin, Sanata Jonah David Jang da wasu mukarraban gwamnatin sa da dama.

A cikin takardar, mun samu cewa mahalarta taron sun tattauna ne akan yadda za su kawo karshen abun da suka kira mamaya da sauran kabilu ke yi masu a jihar, abun da suka ce ba za su lamun ta ba.

Haka zalika a cikin taron dai sun tattauna sosai tare da tsara hanyoyin yadda gwamnan jihar a matsayin sa na daya daga cikin su zai bi wajen dabbaka dukkan tsare tsaren su cikin sirri.Naija.ng.

No comments:

Post a Comment