Sunday, 14 October 2018

Takai ya karbo tutar takara daga Abuja (Hotuna)

Bisa dukkan alamu dai ta tabbata cewar tsohon dan takarar gwamna a jihar Kano, Mallam Salihu Sagir Takai ne dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Wannan na zuwa ne bayan an kwashe lokaci mai tsawo ana fafatawa tsakanin bangaren Sanata Mas'ud El-Jibril Doguwa da ke goyon bayan Takai da kuma bangaren Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke son surukinsa Engr. Abba Yusuf ya zama dan takarar.

Takai ya tafi hedkwatan jam'iyyar PDP da ke Abuja inda ya karbo tutan takarar gwamna kamar yadda wani bibiyar shafin Twitter @mubarakbnyunus ya wallafa a shafinsa.
Wata majiyar ta kuma ruwaito cewar an bawa Kwankwaso kwanaki biyu domin ya zabo wanda zaiyi takara a matsayin mataimakin gwamna a jihar.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment